ha_tn/psa/009/013.md

677 B

dubi yadda waɗanda ke gãba da ni suka wulaƙanta ni

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "ku ga yadda waɗanda suka ƙi ni suke zaluntata" ko "ku ga yadda maƙiyana suka cutar da ni" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kaine wanda zai kuɓutar da ni daga ƙofofin mutuwa

Ana maganar mutuwa kamar birni ne wanda yake da kofofin da mutane suke shiga ta ciki. Idan wani yana kusa da ƙofofin mutuwa, yana nufin cewa zai mutu nan ba da daɗewa ba. Ana maganar hana wani daga mutuwa kamar ɗauke shi daga ƙofar garin. AT: "ku wanda zai iya tsamo ni daga mutuwa" ko "ku da ke iya hana ni mutuwa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)