ha_tn/pro/21/01.md

834 B

Zuciyar sarki kamar tafki ce mai gudanowa a cikin hannun Yahweh

Marubucin yayi magana game da zuciyar sarki kamar dai itace ramin ban ruwa a cikin busasshen yanki wanda mutane ke jagorantar ruwa zuwa shuke-shuke da suke buƙata. AT: "Yahweh yana sarrafa zuciyar sarki kamar yadda mutum ke jagorantar ruwa don ban ruwa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Kowanne mutum na ganin hanyarsa dai-dai ne a idanunsa

Idanu suna wakiltar gani, kuma gani yana wakiltar tunani ko hukunci. Marubucin yayi magana game da abin da mutum yake yi kamar dai mutumin yana tafiya ne a kan hanya. AT: "Kowane mutum yana tunanin cewa abin da ya yi mai kyau ne" ko "Kowane mutum yana yanke hukuncin abin da ya aikata a matsayin mai kyau" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])