ha_tn/pro/16/01.md

1.3 KiB

Shirye-shiryen zuciya na mutum ne

Anan kalmar "zuciya" tana wakiltar tunanin mutum da tunanin sa. AT: "Mutum yana yin shiri a cikin zuciyarsa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

daga harshen Yahweh amsa ke fitowa

Mai yiwuwa ma'anoni su ne 1) Yahweh yayi magana akan amsar sa ga shirin mutum, wanda ma'ana kwatanci ne da cewa Yahweh yana yanke hukuncin sakamakon shirin mutumin ko 2) Yahweh yana bawa mutum damar yin magana game da shirin da yayi. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Dukkan hanyoyin mutum suna da tsarki a ganinsa

Idanu suna wakiltar gani, kuma gani yana wakiltar tunani ko hukunci. Marubucin yayi maganar abin da mutum yakeyi kamar mutumin yana tafiya akan hanya. AT: "Mutum yana tunanin cewa duk abin da yake yi mai tsarki ne" ko "Mutum yana yanke hukunci a kan duk abin da ya aikata da tsarkakakke" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

Yahweh ke auna ruhohi

Anan kalmar "ruhohi" tana wakiltar sha'awar mutane da kuma muradinsu. Marubucin yayi magana game da Yahweh yayin fahimta da hukunta sha'awar mutum da muradinsa kamar yana auna ruhun mutumin. AT: "Yahweh yana hukunta dalilan mutum" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])