ha_tn/pro/04/18.md

661 B

tafarkin adalan mutane kamar fitowar rana ne da ke ta ƙara haskakawa

Marubucin ya kwatanta hanyar mutanen kirki da fitowar rana, ma'ana suna cikin aminci saboda suna da haske don ganin inda suke tafiya. AT: "mutanen kirki suna tafiya akan hanyarsu lafiya domin rana ta wayewa a kanta kuma tana haskakawa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

Hanyar mugu kamar duhu take

Marubucin ya kwatanta hanyar mugaye da duhu, ma'ana koyaushe suna cikin haɗari saboda basu da hasken ganin inda suke tafiya. AT: "Miyagu suna tafiya cikin haɗari a kan hanyar su saboda ba su da hasken da za su iya gani" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)