ha_tn/pro/04/13.md

598 B

Ka riƙe koyarwa, kada ka barta ta kubce

Marubucin yayi maganar mutum yana tuna abin da ya koya kamar "umarni" abu ne da mutum zai iya riƙewa sosai. AT: "Ku ci gaba da yin biyayya ga abin da na koya muku kuma kada ku manta da shi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Kada ka bi tafarkin mugaye kuma kada ka bi hanyoyin masu aikata mugunta

Marubucin yayi maganar ayyukan mutum kamar mutumin yana tafiya akan hanya. AT: "Kada ku aikata abin da mugayen mutane suke yi kuma kada ku shiga ayyukan mutanen da suke aikata mugunta" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)