ha_tn/pro/02/06.md

903 B

daga bakinsa ilimi da fahimta ke fitowa

Anan “baki” yana wakiltar Yahweh ne da kansa ko abin da yake faɗa. AT: "daga Yahweh ne ilimi da fahimta suke zuwa" ko kuma "Yahweh yana gaya mana abin da muke buƙatar sani da fahimta" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Yana tanada sahihiyar hikima domin waɗanda suka gamshe shi

Yahweh yana koyar da hikima ga mutane ana maganarsa kamar hikima wani abu ne wanda Yahweh yake ajiyewa kuma yake bawa mutane. AT: "Yana koyar da ainihin hikima ga waɗanda suka faranta masa rai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

yana tsaron tafarkun adalci

Mai yiwuwa ma'anoni sune 1) adalci kansa ana maganarsa kamar yana hanya. AT: "Allah yana tabbatar da cewa mutane sunyi adalci" ko 2) ana maganar rayuwar mutum kamar dai hanya ce. AT: "Allah yana kiyaye waɗanda ke yin adalci" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)