ha_tn/php/03/17.md

2.1 KiB

Ku zama masu koyi da ni

"yi abin da nake yi" ko kuma "yi rayuwa kamar yadda ina rayuwa"

waɗannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare su

"waɗannan da suna rayuwa kamar yadda nake rayuwa" ko kuma "waɗannan da suna yin abin da nake yi"

mutane da dama suna tafiya

An yi maganar halin mutum kamar mutum yana tafiya a kan hanya. AT: "dayawa suna raye" ko "dayawa suna gudanar da rayuwarsu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

sune waɗanda na ba ku labarin su, yanzu kuma ina faɗa maku har da hawaye

Bulus ya katse abinda yake faɗa da waɗannan kalmomi da suke bayyana "da dama." Za'a iya kai su zuwa forkon ko kuma karshen ayan idan akwai bukata.

ina faɗa muku

"na gaya muku sau da dama"

ina faɗa muku har da hawaye

"ina faɗa muku wannan da matukar baƙin ciki"

kamar makiyan giciyen Almasihu ne

"giciyen Almasihu" a nan yana nufin "shan wahala da mutuwar Almasihu." Maƙiyan giciyen sune waɗanda suke cewa sun gaskata da Yesu amma basu yarda su sha wahala ko ma su mutu kamar yadda Yesu ya sha ba. AT: a wata hanya da ya nuna a zahiri cewa suna gaba da Yesu, wanda ya yarda ya sha wahala ya kuma mutu bisa giciye" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Karshen su hallaka ne

"wata rana Allah zai hallakar da su"

allan su shi ne cikin su

"ciki" a nan yana nufin marmarin annashuwar mutum ta jiki. Kiran sa allahn su a nan yana nufin cewa suna marmarin waɗannan annashuwan fiye da marmarin su yi wa Allah biyayya. AT: "sun fi marmarin abinci da sauran annashuwar jiki fiye da marmarin biyayya ga Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

fahariyar su kuma tana cikin kunyar su.

"kunya" a nan yana madadin yadda ya kamata mutanen su ji kunya amma basu ji. AT: suna fahariya da abubuwan da ya kamata su jawo musu kunya" Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Tunanin su na kan al'amuran duniya ne

"duniya" a nan yana nufin dukan abubuwan da ke ba da annashuwar jiki kuma basu girmama Allah. AT: "Dukan tunanin su game da abinda zai gamshe su ne maimakon abin da zai gamshi Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)