ha_tn/php/03/12.md

2.1 KiB

sami waɗannan abubuwa

waɗannan sun haɗa da sanin Almasihu, sanin ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyar Almasihu, da kasancewa ɗaya da Almasihu a cikin mutuwarsa da tashinsa (3:8).

ko kuma na riga na zama cikakke

"don haka ban riga na zama cikakke ba" ko kuma "don haka ban riga na gama girma ba"

Amma na nace

"Amma ina ta ƙoƙari"

in cafki abin da yake cafkakke na Yesu Almasihu

an yi maganar karbar abubuwan ruhu daga Allah kamar Bulus zai cafke su da hanun sa ne. Kuma Yesu yayi maganar cafke Bulus da hannayen sa AT: "ina iya samun waɗannan abubuwan" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

Ni ma da kaina ban cafke ba tukuna

An yi maganar karban abubuwan daga Allah kamar Bulus zai cafke su da hannun sa.AT: "Duk waɗannan abubuwa ba su zama nawa ba tukuna" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba

kamar yadda mai gudu a wasan tsere baya damuwa da fannin tsere da ya riga ya kammala amma yana mayar da hankali ne ga sauran tsere da ya rage, haka ma Bulus yana magana game da mantawa da ayyukan adinin sa na adalci yana kuma maida hankali a kan tseren rayuwa da Almasihu ya sa a gaban shi domin ya kammala" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor|Metaphor)

Ina nacewa zuwa ga manufar nan in kai ga samun ladar nasara na maɗaukakin kiran Allah cikin Almasihu Yesu

Kamar yadda mai wasan gudu yana nacewa domin nasara, Bulus yana nacewa cikin bauta da kuma rayuwar biyayya ga Almasihu. AT: "ina yin duk abin da na iya don in zama kamar Almasihu, kamar mai gudu da ke tsere zuwa ga karshen layi, domin in zama nashi, kuma Allah ya kira ni zuwa wurinsa bayan na mutu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor|Metaphor)

ƙira daga sama

Ma'anoni masu yiwuwa sune, Bulus yayi maganar zama har abada da Allah kamar Allah zai kira Bulus ya haura 1) zuwa sama kamar yadda Yesu yayi ko 2) hawa zuwa dandali inda masu nasara a wasan tsere suke karɓar sakamako a matsayin misalin saduwa da Allah fuska da fuska da kuma karɓar rai na har abada. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)