ha_tn/php/03/04.md

1.2 KiB

Ko da shike

"duk da haka" ko kuma "amma dai"

ni kaina ina gabagaɗi ga jiki. Idan wani zai iya tunanin gabagaɗi ga jiki, ni na fi shi

A nan Bulus yana cewa in da yana yiwuwa ne Allah ya ceci mutane bisa ga abin da suka yi, da lallai Allah zai cece shi. AT: "Babu wani da zai iya yin abubuwan da yawansu za su kai ya gamshi Allah, amma idan akwai wani wanda zai iyan yin abubuwa da yawansu za su kai ya gamshi Allah, to ni zan yi fiye da haka in kuma ganshi allah sosai fiye da kowa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-hypo)

ni kaina

Bulus ya yi amfani da "kaina" domin jaddadawa. "lallai ni"

Anyi mani kaciya

Za'a iya sa wannan a sifan aiki. AT: "Wani Firist ya yi mani kaciya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

a rana ta takwas

"bayan kwana bakwai da haifuwa ta" (UDB)

Bayahuden Yahudawa

Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "ɗan Bayahude mai iyaye Yahudawa" ko kuma 2) "Bayahude tsantsa"

ga zancen shari'a, Bafarisiye nake.

Bayahude yana iya zama Bafarisiye ne idan mahaifinsa Bafarisiye ne. Amma wannan yana sa wa mutumin alhakin rayuwa a matsayin Bafarisiye, da ba da kai na musamman ga dokar Musa. "a matsayi na na Bafarisiye, na miƙa kai gaba ɗaya ga doka."