ha_tn/php/03/01.md

1.8 KiB

Mahaɗin Zance:

Bulus yana ba da na sa shaida game da lokacin da yake tsananta wa masu bi domin ya gargaɗi yan'uwan sa masu bi game da Yahudawan da za su yi ƙoƙari sa su su bi dokoki na da.

A ƙarshe, 'yan'uwana

"Yanzu muna ci gaba, 'yan'uwana" ko kuma "game da sauran al'amura, 'yan'uwana"

'yan'uwa

Juya wannan kamar yadda yake a 1:12.

yi farin ciki cikin Ubangiji

"yi farin ciki saboda duk abinda Allah ya yi"

abu mai nauyi

baƙin ciki

Waɗannan abubuwa zasu tsare ku

"waɗannan abubuwa" a nan na nufin koyaswar Bulus. Za'a iya ƙara wannan a ƙarshen jumla da ya gabata. AT: "domin waɗannan koyaswar za su kare ku daga masu koyaswar ƙarya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Yi hankali

"yi hattara" ko kuma "yi lura"

karnukan ... miyagun ma'aikata ... masu yanke-yanke.

waɗannan hanyoyi ne daban-daban na bayana ƙungiya guda masu koyaswar ƙarya. Bulus yana amfani ne da magana mai ƙarfi domin ya kai/isad da yadda yake ji game da waɗannan malaman Yahudawa Kirista

yanke-yanke

Bulus yana magana ne game da yin kaciya don ya zagi masu koyaswar karya. Masu koyaswar karyan sun ce Allah zai ceci mutum mai kaciya ne kaɗai, wanda ya yanke loɓa. An bukaci wannan ne a dokar Musa ga dukan mazan Isra'ila. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-hyperbole]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]])

Gama mu ne

Bulus ya yi amfani da "mu" domin ya yi magana game da kansa da dukan masu bi na gaskiya a cikin Almasihu, duk da masu bi na Filibi (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

kaciyar

Bulus ya yi amfani ne da wannan yana nufin masubi a cikin Almasihu waɗanda ba a yi masu kaciya ta jiki ba amma suna da kaciya ta ruhu, wato sun karɓi Ruhu Mai Tsarki ta wurin bangaskiya. "mutanen Allah na gaske"

ba mu da gabagadi a cikin jiki.

"kada ku amince da cewa yanka jiki kawai zai gamshi Allah"