ha_tn/phm/01/17.md

1.6 KiB

Idan ka maishe ni abokin hidima

"idan kayi tunanina a matsayin abokin aiki na Almasihu"

ka mai da shi a kaina

"ka faɗa cewa ni ke rike da basussukan ka"

Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna

"Ni, Bulus, na rubuta wannan da kaina." Bulus ne ya rubuto wannan sashi da hannun sa, saboda Filimon ya sa ni kalmomin daga Bulus ne. Da gaske Bulus zai biya shi.

kada ma a yi zancen

"Ba sai na tunashe ka ba" ko "Ka riga ka sani." Ko da shike Bulus na faɗin cewa bai kamata ya faɗa wa Filimon wannan ba, amma ya cigaba da faɗin hakan. Faɗin hakan ya ƙarfafa gaskiyar abinda Bulus ke faɗa masa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-irony)

ina bin ka bashin kanka

"ina bin ka bashin rayuwar ka." Bulus na faɗin cewa kada Filimon ya ga kamar yana bin Onisimus ko Bulus bashin wani abu domin Bulu na bin Filimon bashi mai yawa. Dalilin kuma shi ne Bulus na bin Filimon bashin ran sa. AT: "kana riƙe da bashi na mai yawa domin na ceci rayuwar ka" ko "abin da na faɗa maka ya ceci rayuwar ka, soboda haka ina bin ka bashin rayuwar ka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu

A nan "hutu" na nufin ta'aziya ko karfafawa. A nan "zuciya" kuma na nufin yanda mutum ke ji, tunani, ko cikin jiki. Bulus ya so Filimon ya ba wa zuciyarsa hutu. AT: "ka karfafa ni a cikin Almasihu" ko "ka ta'azantar da ni a cikin Almasihu" ko "ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu ta wurin karɓar Onisimus" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)