ha_tn/phm/01/10.md

1.9 KiB

ɗana Onisimus

"ɗana Onisimus." Bulus ya yi magana game da abokantakar su da Onisimus kamar yanda uba ya ke ƙaunar ɗansa. Ba wai Onisimus ɗan Bulus ne na asali ba, amma ya karbi koyarwa ta ruhaniya game da Yesu ta wurin Bulus ne, kuma Bulus ya ƙaunace shi. AT: "Onisimus ɗana na ruhaniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Onisimus

Wannan suna "Onisimus" na nufin "riba" ko "mai amfani" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

wanda na zama uba a gare shi sa'anda nake cikin sarƙoƙina

A nan "uba" na nufin cewa Bulus ne ya canza Onisimus zuwa mataki na sannin Almasihu. AT: "wanda ya zama ɗa na ruhaniya a gare ni, na koyar da shi game da Almasihu ya kuma karɓi sabon rayuwa yayinda ina sarƙoƙina" ko "wanda ya zama kamar ɗa a gare ni yayinda ina cikin sarƙoƙina" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

cikin sarƙoƙina ... yayin da ina cikin sarƙoƙi

'Yan kurkuku kunlum na cikin sarƙoƙi. Bulus ya koyar da Onisimus sa'anda yana cikin kurkuku, a cikin kurkuku kuma ya rubuto wannan wasiƙa. AT: "... yayin da ina cikin kurkuku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Na kuma aike shi wurinka

Ya yiwu Bulus ya aiki Onisimus tare da wani mai bi dauke da wannan wasiƙa.

wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai

A nan "zuciya" na nuna shauƙi na mutum. wannan jimla "wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai" na nuna ƙauna da wani ke da shi ga wani. Bulus na faɗin wannan game da Onisimus. AT: "wanda nake ƙauna sosai" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

domin ya rika yi mini hidima a madadin ka

"domin shi zai taimake ni, tun da bazaka kasance a nan ba" ko "domin shi zai iya taimako na a madadin ka"

saboda bishara

Bulus ya shigga kurkuku sabo da ya yi shelar bishara a fili. AT: "sabo da na yi shelar bishara a fili" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)