ha_tn/phm/01/01.md

2.3 KiB

Muhimmin Bayyani:

Sau uku Bulus ya nuna kansa a matsayin marubucin wannan wasiƙar. A fili yake cewa Timoti yana tare da Bulus lokacin rubuta wannan wasiƙar, kuma babu mamaki Timotawus ne ya rubuta wasiƙar lokacin da Bulus yake faɗin kalaman. Bulus ya miƙa gaisuwar sa ga wanɗanda ke ikilisiyar da ke taruwa a gidan Filimon.

Bulus, ɗan sarka saboda Almasihu Yesu, da kuma Timotawus ɗan'uwanmu, zuwa ga Filimon

Mai yiwuwa harshen ka na da wata hanyar ta da take gabatar da marubucin wasiƙa. AT: "Ni, Bulus, ɗan sarka saboda Almasihu Yesu, da kuma Timotawus, ɗan'uwan mu, na rubuta wannan wasiƙa zuwa ga Filimon" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)

ɗan sarka na Almasihu Yesu

"ɗan sarka saboda Almasihu Yesu." mutanen da suka yi tsayanya da wa'azin Bulus sun horas da shi ta wurin jefa shi a kurkuku.

ɗan'uwa

A nan wannan na nufin abokin aiki mabiyin addinin kirista

Filimon, ƙaunataccen abokin aikinmu ... Afiya 'yar'uwanmu ... Arkifus abokin aikin mu a filin daga

wannan kalmar "mu" na nufin Bulus da wanda suke tare. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)

da abokin aiki

"wanda yake kamar mu, yake aikin shelar bishara"

Afiya 'yar'uwanmu

A nan "'yar'uwa" na nufin ita daga zumuntar masubi ne. AT: "maibi ce abokiyar aikinmu Afiya" ko "Afiya yar'uwarmu ta ruhaniya ce" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Arkifus

Wannan sunar mutum ne da ke ikilisiya ɗaya da Filimon. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

abokin aikin mu a filin daga

Bulus ya yi magana a nan game da Arkifus kamar su sojoji ne a filin daga. Yana nufin Arkifus mai kwazo ne kwarai, kamar yadda Bulus kansa mai kwazon shelar bishara ne. AT: "abokin aikin mu jarumin mayaƙi na ruhaniya" ko "jarumin mayaƙi wanda yayi faɗa na ruhaniya tare da mu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku

"Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu shi ba ku alheri da salama." Wannan albarka ne.

Allah Ubanmu

A nan kalmarnan "mu" na nufin Bulus, da waɗanda suke tare, da masu karanta wasiƙar. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

Ubanmu

Wannan muhimmin sunan Allah ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)