ha_tn/num/29/01.md

876 B

Muhimman Bayani:

Yahweh ya cigaba da gaya wa Musa abin da lallai ne mutanen su yi.

wata na bakwai, a rana ta fari ciki watan

"wata na bakwai, a rana ta fari a watan." Wannan na nufin wata na bakwai bisa ga kalandar Yahudawa. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/translate-hebrewmonths]] and [[rc:///ta/man/translate/translate-ordinal]])

yi taro mai tsarki na girmama Yahweh

"taru a wuri ɗaya don su yi wa Yahweh sujada su kuma girmama Yahweh." Maganan nan "taro mai tsarki" na nufin cewa mutanen sun taru don su yi wa Yahweh sujada. Sujada ga Yahweh abu ne mai tsarki.

ta zama ranar da za ku busa ƙahoni

A nan kalman nan "ku" na nufin mutanen Isra'ila wanda suke wakilcin firist. Firist ya busa ƙaho don a fara sujada ko kuwa don a tara jama'ar a wuri ɗaya. AT: "zai zama ranar da firist ya busa ƙahoni" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)