ha_tn/num/21/24.md

954 B

Isra'ila ta faɗa wa

A nan "Isra'ila" na nufin mutanen Isra'ila. AT: "Isra'ilawa sun faɗa wa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

da kaifin takobi

"da wuri mai kaifi na takobin." "kaifin takobin" na nufin mutuwa da kuma hallaka gabaɗaya. AT: " da cin gabaɗayan su da yaƙi " (UDB) (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

karɓi ƙasar su

"ci ƙasar Amoriyawa da yaƙi." A nan kalman nan "su" na nufin Amoriyawan.

mutanen Ammon ... Amoriyawan

"Amoniyawan ... Amoriyawan" ko "mutanen Ammon ... da mutanen Amor." Waɗannan sunayen sun yi kama, amma suna nufin ƙungiyan mutane biyu ne.

ƙayata iyakar

"matuƙar tsaro" (UDB). Isra'ilawan ba su kai wa Amonawan hari ba.

Heshbon da dukkan kauyukanta

A nan "ta" na nufin dangantakan da ke tsakanina birnin Heshbon da waɗannan kauyukan da ke kusa. AT: "Heshbon da kauyukan da ta ke mulki"

Sihon ya ƙwace dukkan ƙasarsa

A nan "sa" na nufin sarkin Mowab.