ha_tn/num/10/35.md

1.2 KiB

Duk sa'ad da sanduƙin ya tashi

A nan an yi magana game da sanduƙin sai ka ce mutum matafiyi. Mutane ne suke ɗaukan sanduƙin. AT: "Duk sa'ad da mutanen da ke ɗaukan sanduƙin sun fara tafiya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

Tashi, Yahweh

A nan maganan nan "tashi" roƙo ne zuwa ga Yahweh don ya yi wani abu, saboda haka, a wannan yanayi, Musa na roƙo shi ya watsar da abonkan găban su. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ka sa maƙiyanka su yi nesa da kai

A nan Musa ya yi magana game da, Yahweh ya sa abokan găban su su rabu da mutanen Isra'ila sai ka ce suna guduwa ne daga gaban Yahweh kansa. AT: "Ka sa waɗanda suke maƙiyanka su yi nesa daga sanduƙin da kuma mutanen ka" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Duk sa'ad da sanduƙin ya tsaya

A nan an yi magana game da sanduƙin sai ka ce mutum matafiyi. Mutane ne suke ɗaukan sanduƙin. AT: "Duk sa'ad da mutanen da ke ɗaukan sanduƙin sun tsaya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

masu yawa dubun dubbai

Wannan na nufin mutanen. An iya bayana ma'anar wannan magana a fili. AT: "da yawan mutanen dubun dubbai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)