1.1 KiB
A watan Nisan
"Nisan" sunan watan farko ne a kalandar Ibraniyawa. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-hebrewmonths)
a shekara ta ashirin ta sarautar Atazazas sarki
"A shekara ta ashirin da Atazazas ke sarki" (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-ordinal)
Sai ya zamana
An yi amfani da wannan kalma a nuna alamar yankewa daga ainihin layin labarin. A nan Nehemiya ya faɗi tushen zance game da yanayinsa a gaban sarki. (Duba: rc://*/ta/man/translate/writing-background)
Amma sarki
"Sai sarkin"
me ya sa fuskarka ta ɓaci
A nan ana nuna Nehemiya ta fuskarsa domin fuska na nuna lamirin wani. AT: "Me yasa ranka ya ɓaci" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)
Hakika wannan damuwar zuciya ce
Wannan na maganar ɓacin ran Nehemiya kamar cewa zuciyarsa ta ɓaci, tunda ana la'akari da zuciya a matsayin cibiyar lamiri. AT: "Kana cikin ɓacin rai sosai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)
Daga nan sai na tsorata sosai
Yayin da Nehemiya ya shirya bada amsa, sai yaji tsoro domin bai san yadda sarki zai ɗauki abin ba.