ha_tn/mrk/15/01.md

1.1 KiB

Mahaɗin Zance:

Da manyan firistoci, da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka Yesu wurin Bilatus, sai suka zarge shi da aikata munanan abubuwa. Da Bilatus ya tambaya ko karan da suka kawo gaskiya ne, Yesu bai amsa shi ba.

suka ɗaure Yesu, suka sa shi gaba

Sun umurta a ɗaure yesu, amma yana iya zama cewa masu tsaro ne suka ɗaure shi suka sa shi gaba. AT: "suka umarta a ɗaure Yesu, sa'annan aka yi gaba da shi" ko kuma "suka umarce masu tsaron su ɗaura Yesu, sa'annan suke sa shi gaba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

suka miƙa shi ga Bilatus

Suka sa aka kai Yesu ga Bilatus, sa'annan suka bar shi yă bi da Yesu.

haka ka ce

Wannan na iya nufin 1) ta wurin faɗin haka, Yesu yana cewa Bilatus ne ke ce da shi Sarkin Yahudawa ba Yesu ba. AT: "Ai kai da kanka ne ke ce haka" ko kuma 2) ta wurin faɗin haka, Yesu na nufin cewa shi ne Sarkin Yahudawa. AT: "I, yadda ka faɗa, Ni ne" ko kuma "I, haka ne yadda ka faɗa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

suka kawo zargi iri iri a kan Yesu

"suna zargen Yesu da laifuffuka iri iri" ko kuma "suna cewa Yesu ya aikata munanan abubuwa masu yawa"