ha_tn/mrk/04/10.md

1.2 KiB

Sa'adda Yesu yake shi kadai

Ba wai wannan na nufin cewa Yesu yana nan gabaɗaya shi kaɗai ba; maimakon haka, abin nufi shine, lokacin da taron sun tafi, Yesu kuma na tare da sha biyun da wasu masubinsa.

an ba ku

AT: "Allah ya ba ku" ko "Na ba ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

waɗanda ba su cikinku

"amma waɗanda ba sa cikin ku." Wannan na nufin dukkan mutanen da ba sa cikin sha-biyun ko sauran masubi Yesu na kusa.

komai sai a cikin Misalai

Ana iya faɗin cewa Yesu ya ba wa mutanen misalai. AT: "Kowane abin da na faɗa, na yi shi cikin misali" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)

don gani da ido ... sun ji

Ana ɗaukan cewa Yesu yana magana game da mutane suna ganin abubuwan da ya nuna masu suna kuma jin abin da ya gaya masu. AT: "sa'ad da suna ganin abin da nake yi ... sa'ad da suna jin abin da nake faɗa (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

sun gani, amma ba su gane ba

Yesu yana magana game da fahimtar mutane ga abin da suka gani kamar a zahiri suna gani ne. AT: "sun gani ba su kuma gane ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

za su juyo

"juyo wurin Allah." Anan "juyo" na nufin "tuba," AT: "za su tuba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)