818 B
818 B
kiwon mutanenka da sandarka, wato, garken mallakarka
Mika yana addu'a ga Yahweh, yana rokonsa ya kare jama'arsa Isra'ila kuma. A nan "sanda" tana nufin shugabanci da jagorancin Allah, kamar yadda makiyayi yake amfani da sanda wajen bi da tumakinsa da kuma kare su.
zaune su kadai a kurmi
Mika yana nufin cewa wadansu cikin mutanen suna zaune a wurinda kasar ba ta da amfani, kuma an yanke su daga sauran jama'a, ba za su iya samu kayayyakin da suke bukata a saukake ba.
Bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad
Wadanan yankunan sun yi fice a matsayin kasa mai kyau don girmar da abinci. Saboda haka, Mika yana rokon karin fadadawa ta yankin, wanda aka rasa a da saboda abokan gaba sun mamaye.
kamar a kwanakin da
Wannan yana iya nufin sa'adda Sulemanu yake sarki.
Zan nuna
A nan "zan" yana nufin Yahweh.