ha_tn/mic/07/07.md

431 B

Amma ni

A nan "ni" yana nufin Mika.

kada ku yi murna a kaina

Ba ga kansa kadai Mika yake magana ba. Yana nufin kada abokin gaba ya yi murna a kan abin da ke faruwa da jama'ar Isra'ila.

Sa'ad da na zauna a cikin duhu, Yahweh zai haskaka ni

Mika yana nuni da masifar da ke zuwa ga jama'ar Isra'ila a matsayin "duhu". Yana nufin cewa, ko da Allah ya bar abokan gaba sun zo sun hallaka su yanzu, zai zo ya cece su nan gaba.