ha_tn/mic/05/04.md

887 B

Muhimmin Bayani:

Wadannan ayoyin sun ci gaba da bayyana mai mulkin daga Baitalami.

Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da karfin Yahweh

AT: "Zai jagoanci jama'arsa da karfin Yahweh".

da daukakar sunan Yahweh Allahnsa

AT: "cikin karfin ikon Yahweh Allahnsa"

Za su kuwa zauna

A nan, "su" yana nufin mutanen Isra'ila. Ana nufar kalmar "Isra'ila" ko "Yerusalem".

gama zai zama mai girma cikin duniya duka

Wannan yana nufin cewa, nan gaba dukkan mutane daga kowace al'umma za su girmama mai mulkin Yerusalem.

Zai zama salamarmu

A nan "mu" yana nufin Mika da jama'ar Isra'ila. AT: "Zai zama mai kawo salama"

makiyaya bakwai da shugabanni takwas a kan maza

A nan "makiyaya" yana nufin "masu mulki". Haka kuma, za ka iya kara bayanin kasan shafi mai cewa, "Lambobin nan 'bakwai' da 'takwas', tare suna nufin cewa za a sami yawan shugabannin da za su biya bukata".