ha_tn/mic/05/02.md

1.2 KiB

Amma ke, Betlehem ta Ifrata

Yahweh yana magana da mutanen wannan garin kamar suna wurin suna sauraro.

Ifrata

Wannan zai iya zama ko sunan wani yanki ne a inda Betlehem take ko kuma wani suna ne kuma na Betlehem ko yana bambanta wannan Betlehem da wata. Betlehem tana da nisan kusan mil shida kudu da Yerusalem. Garin Sarki Dauda kenan. Masu fassara suna kara wannan bayanin kasan shafin: "Sunan nan, 'Ifrata' yana nufin 'ba da amfanin 'ya'ya'".

Duk da cewa ke ce 'yar karama a cikin kabilar Yahuza

Wannan yana nufin Allah zai yi manyan al'amra ta hannun dan karamin gari mara tasiri.

komo wurina

A nan "na" yana nufin Yahweh.

Wanda asalinsa tun fil'azal ne, daga har adaba

Wannan yana nufin mai mulkin zai zo daga zuriyar asali ta Sarki Dauda. Kalmomin "tun fil'azal" da "daga har abada" suna nufin abu daya ne, kuma suna jaddada dadewan wannan zuriyar a tarihi.

Domin haka Allah zai yashe su

"Saboda haka Allah zai manta da jama'ar Isra'ila".

sai lokacin da wacce take nakuda ta haihu

Wannan yana nufin lokacin da za a haifi mai mulkin, dan kankanin lokaci.

sauran 'yan'uwansa

"sauran 'yan'uwansa Isra'ilawa". Wadannan su ne Isra'ilawa da suke bauta. A nan "'yan'uwansa" suna nuni da yaron da zai zama mai mulki.