ha_tn/mic/03/12.md

615 B

Saboda ku

A nan, "ku" na nufin firistoci, annabwa, da shugabanni na ayar da ta gabata.

za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma za ta zama tsibin kufai, dutsen inda haikali yake zai zama kurmi.

Mika yana nufin cewa za a hallaka Urushalima gaba daya. Babban birni mai yawan jama'a zai zama kufai, ya zama kamar gona ko kurmi.

za a nome Sihiyona kamar gona

Bayan an hallakar da ita, Urushalima za ta zama wurin noma. AT: "Wadansu za su nome Sihiyona kamar gona".

dutsen in da haikali yake zai zama kurmi

Har harabar haikali ma ba zai ta tsira ba. Shugabannin sun lalata ta, za kuma a hallaka ta.