ha_tn/mat/27/03.md

1.2 KiB

Muhimmin Bayani:

Wannan abin ya faru a bayan shari'ar Yesu a gaban majalisar shugabannin adinin Yahudawa, amma ba mu san ko ya faru kafin shari'a ko lokacin shari'ar Yesu a gaban Bilatus ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-events)

Sa'adda Yahuza

Idan harshenku na da wata hanyar nuna cewa an fara sabon labari, za ku so ku iya amfani da shi a nan.

cewa an zartarwa Yesu hukunci

AT: "cewa shugabannin Yahudawa sun hukunta Yesu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

azurfar talatin

Wannan ne ƙudin da firistoci suka ba wa Yahuza don ya bashe Yesu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 26:15.

mara laifi

Wannan ƙarin magana ne da na nufin mutuwar mai mara laifi. AT: "mutumin da bai cancanci mutuwa ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Ina ruwan mu?

Shugabannin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su nanata cewa ba su damu da abin da Yahuza ya faɗa ba. AT: "Wannan ba damuwar mu bane!" ko "Wannan damuwar ku ne!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

jefar da kwandalolin azurfar a cikin haikalin

AT: 1) ya jefar da kandalolin azurfar a cikin farfajiyar haikalin, ko 2) ya na tsaye a cikin farfajiyar haikalin, sai ya jefar da kwandalolin azurfar a cikin haikalin.