ha_tn/mat/11/01.md

1.5 KiB

Muhimman Bayani:

Wannan wani bangare ne daga cikin farkon labarin da Matiyu ya bayana yadda Yesu ya yi magana game da Yahaya Mai Baftisma ga almajiransa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/writing-newevent)

Bayan wannan

Wannan magana ya kai mu daga koyaswar Yesu zuwa ga abin da ya faru a gaba. AT: "Sa'anan kuma" " ko "Bayan haka"

ya gama gargaɗad

"ya gama koyar" ko "ya gama bada umurnin"

almajiransa sha biyun

Wannan na nufin mazanai goma sha biyun da Yesu ya zaɓa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-numbers)

cikin biranensu

A nan "su" na nufin Yahudawa gabakiɗaya.

Da

Wannan kalman alama ce ta kaucewa daga ainihin kan labarin. Anan Matiyu ya fara bada sabuwar gangaren labarin.

Da Yahaya Mai Baftisma ya ji daga kurkuku game da

"Lokacin da Yahaya, wanda ke cikin kurkuku, ya ji game da" ko kuwa "Sa'ad da wani ya gaya wa Yahaya, wanda ke a kurkuku, game da." Kodashike, Matiyu bai gaya wa masu karatunsa cewa Sarki Hiridus ya kulle Yahaya a kurkuku ba, ainihin wanda ya rubuta masu suna sane da labarin sun kuma san ainihin zance anan. Matiyu zai kara yin bayani nan gaba game da Yahaya Mai Baftisma, saboda haka, zai fi kyau kada a bayana shi anan.

sai ya aika sako ta wurin almajiransa

Yahaya Mai Baftisma ya aike almajiransa da sako zuwa ga Yesu.

Ya ce masa

"sa" na nufin Yesu.

Shin, Kai ne mai zuwa

"Kai ne wanda muke sa sammanin zuwansa." Wannan a wani hanya, na nufin Mai Ceto ko Almasihu.

mu sa ido ga wani

"Mu yi sammanin wani dabam" Kalman nan "mu" na nufin dukkan Yahudawa ba almajiran Yahaya ba.