ha_tn/mat/10/05.md

1.0 KiB

Sha biyun nan da Yesu ya aika

"Yesu ya aika waɗannan mutane sha biyu" ko "waɗannan mutane sha biyun nan ne Yesu ya aiko":

aiko

Yesu ya aike su don wata dalili.

Ya umurce su

"Ya gaya masu abin da za su yi" ko "ya umurce su"

batattun tumaki na gidan Isra'ila

Wannan ƙarin magana ne da na ƙwatanta dukka al'umman Isra'ila da tumakin da sun bazu daga makiyayinsu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

gidan Isra'ila

Wannan na nufin al'umman Isra'ila. AT: "mutanen Isra'ila" ko "zuriyar Isra'ila" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Sa'ad da kun tafi

A nan "kun" jam'i ne kuma na nufin manzane goma sha biyu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-you)

Mulkin Sama ya kusato

Jumlar "Mulkin Sama" na nufin mulkin Allah kamar sarki. Wannan jumla na cikin littafin Matiyu ne kadai. Idan ya yiwu, yi amfani da kalmar "sama" a cikin juyinku. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 3:2. AT: "Allahn mu a sama ya yi kusa ya nuna kansa a matsayin sarki" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)