ha_tn/mat/07/03.md

1.5 KiB

don me kake duban ... idon ɗan'uwa, amma gungumen da ke a naka idon ba ka kula ba?

Yesu ya yi amfani da tambaya ya tsautawa mutanen domin suna mai da hankali a zunubin wasu, ba sa kula da nasu zunubin. AT: kuna duban ... idon ɗan'uwa, amma ba ku lura da gungumen da yake a naku idon." ko "kada ku dubi ... idon ɗan'uwa, kuma kula da gungumen da yake naka idon." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ɗan hakin da ke idon ɗan'uwanka

Wannan na nufin ɗan laifi da ɗan'uwa maibi ya aikata mara muhimmanci. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ɗan haki

"yayi" ko "sartse" ko "ɗan ƙura." Yi amfani da sunan ɗan karamin abu da ya saba fadi a idonun mutum.

ɗan'uwa

duk inda aka yi amfani da kalmar "ɗan'uwa" a 7:3-5, ana nufin ɗan'uwa maibi ne ba ɗan'uwan haifuwa ko maƙwabci ba.

gungumen da yake a naka idon

Wannan na nufin babban laifin da mutum a aikata. Gungume ba iya shigan idon mutum, Yesu ya yi amfani da wannan domin ya jaddada cewa mutum ya mayar da hankalinsa akan babban laifinsa kafin ya shiga harkar kananar laifofin wani. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-hyperbole]])

gungume

sashi ne mafi girma a itacen da aka yanka

yaya za ka iya ce ... naka idon?

Yesu yayi amfani da wannan tambaya domin ya kalubalence mutane su sa hankalinsu a nasu zunuben kafin su sa hankalin su a zunuben wani. AT: "kada ka ce ... idon ka." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)