ha_tn/mat/05/46.md

1.3 KiB

Idan kuna ƙauna waɗanda ... wani lada ne kuke da shi?

Yesu yayi amfani da tambaya dommin ya koyad da mutanen cewa idan masoyansu kadai suke ƙauna, ai ba wani muhimmin abu ne da Allah zai saka musu ba. AT: "Gama in kuna ƙaunar iyakar wanɗanda ... ba ku samu ko wani lada ba." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Ba haka masu karɓar haraji ma suke yi ba?

Yahudawa na duban masu karɓar haraji a matsayin masu zunubi ƙwarai. Yesu yayi amfani da wannan tambaya ya tunashe su cewa ai ko masu karɓar haraji ma suna ƙaunar masoyansu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

In 'yan'uwanku kaɗai ku ke gai da su, me kuke yi fiye da wasu?

Yesu yayi amfani da tambaya dommin ya koyad da mutanen cewa idan 'ya'uwansu kaɗai suke gayarwa, ai ba wani muhimmin abu ne da Allah zai saka musu akai ba. AT: "Idan 'ya'uwanku kaɗai kuke gayarwa, ba kuwa yin komai fiye da waɗansu." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

gaisuwa

Wannan hanyar nuna marmari ne domin lafiyar mai jin.

ko al'ummai ma, ba haka suke yi ba?

Yahudawa na duban al'ummai a matsayin masu zunubi sosai. Yesu ya yi tambaya ya tunashe su cewa ai al'ummai ma suna gai da 'yan'uwansu. AT: "ai ko al'ummai suna gai da mutanensu." Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)