ha_tn/mat/05/40.md

958 B

taguwa ... mayafi

Ana sa "tuguwa" a jiki ne, kamar riga mai nauyi. "mayafi" kuwa ya fi taguwa daraja, ana sa wannan akan taguwa ne domin dumi, kua akan yi amfani da shi kamar bargo wajen barci.

ka bar mutumin ya karba

"ka kuma ba mutumin"

Duk wanda

"Ko wanene." mahalin wannan maganar na nuna cewa ya na magana ne game da sojojin Roma. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

mil guda daya

Wannan na nufin takawa dubu, domin wannan ne iyakar tafiyar da sojan Roma ke da ikon tilasta wani ɗauka masa abu bisa ga doka. Idan ba a gane kalmar "mil" sosai ba, ana iya fasara wannan kamar "kilomita" ko "bisa nisa."

tare da shi

wannan na nufin ga wanda ya tilasta ka yin tafiya.

yi tafiya dashi mil biyu

"yi tafiyar da ya tilasta maka, ka kuma kara wani mil." Idanba a gane kalmar "mil" ba, yi amfani da fasarar "kilomita biyu" ko kuma "hada nisar tafiyar sau biyu."

kada ka juya

"kada ka hana ba da rance." AT: "rantar wa"