ha_tn/mat/05/33.md

1.4 KiB

kuma, ku

"ku kuma" ko "ga wani misali. ku"

an faɗa wa mutanen dã

AT: "Allah ya faɗa wa mutanen zamanin da ya wuce" ko "Musa ya faɗa wa kakani tun da daɗewa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kada kã rantse akan ƙarya, amma ka cika wa'adin ka ga Ubangiji.

"kada ka ɗauka alkawarin yin abu sa'an anan ka ki yi. Amaimako sai ka aikata abu da ka ɗau alkawari ga Ubangiji cewa za ka yi"

kada ma ku rantse sam ... birnin babban Sarki

A nan Yesu na nufin cewa kada wanda suke ɗaukan alkawari ko faɗin gaskiya su rantse da wani abu. Wasu suna koyar cewa idan mutum ya rantse da Allah to wajibi ne ya cika, amma idan rantsuwar ga wani abu ne kamar samaniya ko ƙasa, to ba shi da wani illa sosai idan bai cika ba. Yesu na cewa rantsuwa da samaniya ko ƙasa ko Urshalima na da muhimminci ɗaya da rantsuwa da Allah, domin Allah ne ke da dukka abubuwa.

kada ma ku rantse sam

"kada ku ɗauki rantsuwa ko kadan" ko "kada ku rantse da kowani abu"

kursiyin Allah ne

Domin Allah na mulki da ga sama. Yesu na maganar sama kamar sama kursiyi ne. AT: "da ga nan ne Allah ke mulki" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ita ce matashin ƙafarsa

Wannan maganar na nufin cewa ƙasa ma na Allah ne. AT: "ta na kamar matashi ne da sarki ke sa ƙafarsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ita ce birnin babban Sarki

"domin ita ce birnin Allah, babban Sarki"