ha_tn/mat/03/10.md

2.6 KiB

mahaɗin zance

Yahaya mai Baftisma ya cigaba da tsautawa Farisawa da Sadukiyawa.

Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.

Wannan na nufin Allah na shirye ya hukunta masu zunubi. Za a iya bayana wannan ta wata hanya. AT: "Allah na shirye da gatarinsa ya sare duk itãcen da ta ke ba da mumunan 'ya'ya ya kuma kona ta" ko kuma "Kamar yadda mutum ke shirya gatarinsa domin ya sare itãcen da ke ba da 'ya'ya marasa kyau domin ya kone ta, haka Allah ke shirye domin ya hukunta ku sabili da zunubanku" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

domin tũba

"nuna cewa an tũba"

Amma mai zuwa baya na

Yesu shine mutumin da ke zuwa bayan Yahaya.

ya fi ni girma

"yana da muhimmanci fiye da ni"

Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta

Ana kamanta baftisman da Yahaya ke yi da ruwa da kuma baftisma da ke zuwa na wuta. Wannan na nuna cewa baftisma Yahaya alama ce na tsaftace mutane daga zunuban su. Baftismar Ruhu mai Tsarki da wuta kuma shine ke da gaskiyar ikon wanke mutane daga zunubansu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Kwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai

Wannan na kwatanta yadda Almasihu zai ware adalai da marasa adalci kamar yadda mutum ke ware alkama da ɓuntu. AT: "Almasihu na kamar mutumin da kwaryar shiƙarsa na hannunsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Kwaryar shiƙarsa na hannunsa

Anan "na hannunsa" na nufin mutum da ke shirye domin aiki. AT: "Almasihu na rike da Kwaryar shiƙarsa domin yana shirye" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Kwaryar shiƙarsa

Wannan kayan aikin sheke alkama ne domin a ware alkaman da ɓuntu. Ana jefa su sama amma alkaman na saukowa, sai iska ya kwaso ɓuntun zuwa wata gefe. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-unknown)

share masussukarsa sarai

Almasihu na kamar mutumin da ke rike da Kwaryar shiƙarsa domin ya share masussukarsa.

masussukarsa

"filinsa" ko kuma "filin ƙasa inda yake ware hatsin daga ɓutun"

tãra alkamarsa ya sa a rumbunsa, ... ƙona ɓuntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.

Wannan na nuna yadda Allah zai ware adalai daga miyagu mutane. Adalai kuwa za su sama kamar yadda manomi ke tãra alkama a rumbu, sai Allah ya ƙone mutanen da ke kamar ɓuntu da wutan da ba za a iya kashewa ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ba za a iya kashewa ba

AT: "ba za ta taba karewa ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)