ha_tn/mat/03/07.md

1.5 KiB

Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya...

A nan " 'ya'ya" na nufin "yanayin halayya kamar." Macizai masu dafi na ba hoton miyagu ko mugunta. AT: "Ku mugayen macizai masu dafi! wa ya" ko kuma "Ku mugaye kamar macizai masu dafi! Wa ya" (dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

wa ya kwaɓe ku, ku guje wa fushi mai zuwa?

Yahaya ya yi amfani da tambaya domin ya tsautawa farisawa da sadukiyawa wanda suna so ya yi masu baftisma domin su gujewa hukuncin Allah, amma ba su so su daina aikata zunubi. AT: "ba za ku iya guje wa fushin Allah haka ba." ko kuma "kada ku yi tunani cewa za ku gujewa fushin Allah wai domin na yi maku baftisma." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

guje wa fushi mai zuwa

kalmar "fushi" na nufin hukuncin Allah domin fushinsa na zuwa kafin hukuncin. AT:"guje wa hukunci da ke zuwa " ko kuma "kuɓuta daga hukucin Allah a gare ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tũbanku

maganar "ba da 'ya'ya" na nufin halayyan mutum. AT: "Bari ayukkan ku su nuna cewa tũbanku na gaskiya ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu

"Ibrahim kakanmu ne" ko kuma "mu zuriyar Ibrahim ne." Shugabanin Yahudawa na tunani cewa Allah ba zai hukuntasu ba domin su zuriyar Ibrahim ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Domin ina gaya maku

Wannan na kara karfin maganar da Yahaya zai yi.

Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan.

Allah yana da iko ya wa Ibrahim zuriyar ta jiki daga duwatsun nan"