ha_tn/mal/04/01.md

2.3 KiB

duba

"sa ido" ko "saurara" ko "maida hankali kan abin da zan fada muku"

rana tana zuwa ... kone kamar tattaka

Ana maganar masifar da ke abkuwa a wannan lokacin kamar ranar kanta tana konewa. Akan yi maganar hukuncin Allah kamar wuta ne.

masu girmankai ... mugaye

Fassara wadannan kalmomin kamar yadda ka yi a 3:13

dukkan masu girmankai, da mugaye za su kone kamar tattaka

Ana maganar wadannan mutane kamar za su zama busassun itatuwa da suka cancanci konewa kawai. A Littafi Mai Tsarki an saba maganar utane kamar su itatuwa ne ko shuke-shuke. AT: "dukkan masu girmankai da dukkan mugaye za su kone kamar busassun itatuwa"

Ranar da ke zuwa za ta kone su kurmus

A nan, "ranar" tana nufin al'amuran da za su faru a ranar nan. AT: "A ranar nan, zan kone su kurmus"

babu saiwa ko reshe da zai rage

Wannan furcin ya ci gaba da magana kan mutanen kamar su shuke-shuke ne ko itatuwa. Saboda haka, hana saiwowi da rassa yana nufin an kashe su gaba daya. AT: "babu abin da zai rage"

ku da kuke tsoron sunana

A nan, "sunana" yana nufin Yahweh kansa.

rana ta adalci za ta fito da warkarwa a fukafukinta

Wannan yana iya nufin 1) Yahweh, wanda kuma adali ne, zai zo ya warkar da jama'arsa a wannan ranar, ko 2) a wannan ranar, Yahweh zai bayyana adalcin mutanensa, ya warkar da su.

warkarwa a fukafukinta

Ma'anar tana iya zama 1) ana maganar warkar da wani kamar wani abu ne da rana take dauka tana kai wa mutane a fukafukinta, ko 2) warkarwar tana faruwa a karkashin fukafukin, wato, cikin tsaron da Allah yake ba wa mutanensa.

fukafuki

An aba, a yankin Gabashi a zamanin da, a yi maganar rana kamar tana da fukafuki wanda take tafiya da su a sararin sama. Ma'ana tana iya zama 1) ana maganar haske mai rayarwa wadda rana take bayarwa kamar fukafukinta ne, ko 2) ana cewa fukafukin suna kare mutanen Allah, don su ba su salama da tsaro.

Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan marukan da aka fishe su daga garke

A nan, ana maganan fansassun jama'ar Yahweh kamar sun zama 'yan marukan da aka sake daga garkensu, aka bar su su fita kiwo.

Za ku tattake mugaye, gama za su zama kamar kura a karkashin kafafunku

A nan, ana maganar nasarar mutanen Allah kamar suna tafiya ne a kan konannun gawawwakin abokan gabansu.

za su zama kamar kura

Ana maganar abokan gaban Isra'ila kamar sun kone sun zama toka. Duba: 4:1