ha_tn/mal/03/13.md

1.4 KiB

Muhimmin Bayani:

Waɗannan ayoyin suna fara wani sabon sashe a cikin littafin. A nan, Yahweh yana magana ne da jama'ar Isra'ila.

Kalmominku a kaina suna da karfi

A nan, "karfi" yana nufin "tsanani" ko "mugu". Kuma, "kalmominku" yana nufin "Abin da kuka fada". AT: "Abin da kuka fada game da ni yana mugu ne"

Me muka ce a kanka?

Mutanen suna wannan tambayar don su nuna cewa ba su fadi komai a kan Allah ba. Za a iya fadin wannan a matsayin magana. AT: "Ba mu fada wa juna komai a kanka ba".

Ina mafanin a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi tafiya ta baci saboda ayyukan da muka yi wa Yahweh Mai Runduna?

Mutanen suna yin wannan tabayar a tsakaninsu da manufar wata magana. AT: "Babu amfani ma yadda muka kiyaye dokokinsa, muka yi tafiya cikin nadama a gaban Yahweh Mai Runduna".

tafiya ta baci saboda ayyukan da muka yi wa Yahweh Mai Runduna

A nan, "tafiya ta baci" tana nufin "nuna halin nadama", mai yiwuwa domin nuna bakin cikin zunubansu.

gaban Yahweh Mai Runduna

A nan, wannan furcin yana nufin Allah yana sane da wabin da mutanen suke aikatawa.

muna kiran masu girmankai masu albarka

A nan a kira mutum "mai albarka" yana nufin an albarkace shi. AT: "muna cewa masu girman kai suna da albarka"

muna kiran masu girmankai masu albarka

Za a iya fadin wannan kai tsaye. AT: "muna cewa masu girmankai suna jin dadi"

tsira

Wato, "sun tsira daga hukuncin Allah".