ha_tn/mal/03/06.md

818 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh ya ci gaba da magana da jama'ar Isra'ila.

ba ku kare ba

"ba ku hallaka ba"

Daga kwanakin kakanninku kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba

Ana maganar rashin biyayya ga dokokin Allah kamar juyawa daga gare su ne. AT: "Kun yi rashin biyayya da dokokina tun zamanin kakanninku"

Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku

A nan, ana maganar kaunar juna da rike amanar juna kamar komowa ne ga juna. AT: "Ku kaunace ni, ku girmama ni, zan kuwa taimake a kowane lokaci"

Kaka za mu koma?

Mutanen suna yin wannan tambayar don su nuna cewa ba su daina yi wa Allah biyayya ba. Za a iya fadin wannan a matsayin magana. AT: "Ba mu taba bjirewa daga gare ka ba, saboda haka kaka za mu dawo wurinka" ko "Ba mu taba kauce maka ba, don haka babu amfani ka yi mana magana cewa mu dawo wurinka"