ha_tn/mal/03/04.md

1005 B

Muhimmin Bayani:

Malakai ya ci gaba da magana a aya hudu, amma Yahweh ya fara magana kuma a aya biyar.

hadayun Yahuza da Yerusalem

A nan, "Yahuda" da "Yerusalem" suna nufin mutanen waɗannan wuraren. AT: "hadayun da mutanen Yahuda da Yerusalem suke kawowa"

kamar yadda yake a zamanin da, a shekarun da

Waɗannan kalamai biyu suna nufin kusan abu daya, kuma suna jaddada cewa a da hadayu suna karbuwa a gun Yahweh. AT: "kamar yadda yake a da can"

Za zo wurinku do shari'a

A nan, "shari'a" tana nufin aikin hukuntawa. AT: "Sa'annan zan zo wurinku domin in shar'anta ku"

zaluntar ma'aikata a kan albashinsu

"masu sa ma'aikacin da suka dauka ya sha wahala ta wurin kin biyansa kudin aikinsa"

kwarar baki

Wato, tauye wa bako hakkinsa. Ana maganar tauye hakkokin mutane kamar wani yana korar su ne daga gare shi. Mai yiwuwa maganar tana nufin korar wani wanda ya zo don a maida abin da ba daidai ba ya zama daidai. AT: "hana wa bakin da ke zaune a Isra'ila hakkokin da ya kamata su samu"