ha_tn/mal/03/01.md

2.8 KiB

Muhimmin Bayani:

Yahweh ya fara magana kuma da jama'ar Isra'ila a aya ɗaya, amma annabi Malaki ya fara magana a aya biyu.

Duba

"Sa ido" ko "Saurara" ko "Maida hankali ga abin da zan fada muku"

zai shirya mini hanya

A nan, ana maganar shriya mutane domin marabtar Yahweh kamar ana gyara wata hanya don Yahweh ya yi tafiya a kai.

Sa'annan Ubangiji, wanda kuke nema ... Manzon alƙawarin, wanda kuka sa zuciyar zuwansa

Waɗansu juyi na zamani sun fassara wannan da manufar cewa wadannan maganganu biyu suna nufin mutum daya. Sauran fassarorin zamani sun bar wannan tambayar babu cikakken bayani. Muna shawarta cewa fassarori su bar wannan batun a bude, kamar yadda yake a ULB da UDB.

Manzon alƙawarin

Kusan dukkan juyi sun bar wannan maganar a bude. Amma masu fassara za su bukaci su bayyana sosai dangantakar da ke tsakanin "manzo" da "alƙawarin". UDB ya gabatar da "manzon" a matsayin wanda aka yi alƙawarta ta wurin alƙawarin da Yahweh ya yi da Isra'ila. Wani zabi kuma shi ne a gabatar da manzon a matsayin wanda zai tabbatar da alƙawarin ko ya yi shelar sabon alƙawarin.

Amma, wa zai iya jure da ranar zuwansa? Wa kuma zai iya tsayuwa sa'adda ya bayyana?

Wannan salon tambayar tana nufin cewa babu wanda zai iya tayayya da Yahweh sa'ad da ya zo. Za a iya hada su cikin magana guda. AT: "Amma, babu wanda zai iya tsayayya da Yahweh sa'adda ya zo ya shar'anta su".

ranar zuwansa

A nan, "rana" tana nufin "lokaci". AT: "lokacin da ya zo"

zai iya tsayawa

A nan tsayawa tana wakiltan tsayayya da hari ko tuhumar wani.

Zai zama kamar wutar da suke bauta karfe, kamar kuma sabulun salo

Wannan maganar ta ba da dalilin da ya sa babu wanda zai iya tsayayya da Allah sa'adda ya zo. Ikon Allah na hukunta mutanen da kuma hana su zunubi, ana maganarsa kamar ikon sabulu mai karfi na tsaftace tufafi, ko ikon wuta na narkar da abu. Waɗannan hanyoyi ne na cewa ikon Allah na yin waɗannan abubuwa ya wuce a yi tsayayya da shi.

Zai tsarkake 'ya'yan Lebi

Gafarta wa 'ya'yan Lebi da kuma shawo kansu don su daina zunubi, ana maganarsa kamar tace karfe. AT: "kuma zai tsautar da 'ya'yan Lebi, ya gafarta musu son su yi zunubi"

'ya'yan Lebi

A nan, "'ya'ya" na nufin zuriya. Zuriyar maza na Lebi su ne firistoci da ma'aikata a haikali.

Zai zauna

A nan, zama yana nufin aikin makeri, wanda yakan zauna domin ya tace zinariya ko azurfa. Yana kuma nufin aikin sarki, wanda yake zama domin ya yi wa mutane hukunci ya ba da doka.

ya tace su kamar yadda ake yi wa zinariya azurfa

A nan, ana maganar jawo hankalin mutanen don su daina zunubi kamar makeri ne yake kara tace zinariya da azurfa.

za su kawo wa Yahweh hadayun da suka dace

A nan, "suka dace" na nufin "hadayun da aka yi sanadiyar sahihin muradin yi wa Allah sujada". AT: "za su kawo hadayu karbabbu ga Yahweh domin su yi wa Yahweh sujada"