ha_tn/mal/02/17.md

959 B

Kun gajiyar da Yahweh

Ana maganar Yahweh kamar halin mutum yana iya gajiyar da shi, amma Allah ba zai gaji da a jiki ko a zuci ba. Mai yiwuwa wannan maganar tana nufin cewa Yahweh ya ji fushi ko ya fusata. AT: "Kun yi wa Yahweh laifi".

Kaka muka gajiyar da shi?

An nufi wannan tambayar don musunta cewa mutanen sun aikata wani abin da ba daidai ba. Za a iya furta wannan a matsayin magana. AT: "Hakika, ba mu gajiyar da shi ba".

ta wurin cewa

Cikakkiyar maganar ita ce, "Kun gajiyar da shi ta wurin cewa". Wannan ita ce amsar annabin ga wannan tambayar.

a gaban Yahweh

A ann, "a gaban Yahweh" yana nufin "ra'ayin Yahweh".

Ina Allahn adalci yake?

Firistoci suna yin wannan tambaar domin su nuna cewa ko dai Yahweh ba ya kula ko mutanen suna aikata mugunta ko a'a, ko kuma cewa ba ya hukunta masu aikata mugunta. AT: "Hakika, Allah ba ya hukunta masu mugayen mutane".

Allahn adalci

Allah da yake hukunta masu aikata mugunta cikin adalci.