ha_tn/mal/02/13.md

775 B

Muhimmin Bayani:

Malakai ya ci gaba da magana da 'yan'uwansa Isra'ilawa.

Kuna cika bagaden Yahweh da hawaye

Wannan wata hanyar zugugata yadda masu sujada sukan yi ta kuka sa'adda suke yin addu'ar neman taimako daga Yahweh. An nufi wannan maganar da bayyana rashin karbuwar sujadar karyar da suke yi a gun Yahweh.

da kuka, da kururuwa

Kalmomin "kuka" da "kururuwa" suna da ma'ana kusan daya, kuma suna nuna tsananin kuka. A.T: "da kuka mai zafi".

ba zai kalli hadayun ba

A nan, duba kallon kyauta yana nufin karbar ta da kuma nuna tagomashi ga wanda ya bayar.

ba zai kalli hadayun ba

Wannan yana nufin cewa, wadanda suke kuka a bagaden Yahweh sun mika masa hadayu.

daga hannunku

A nan, "hannu" yana nufin mutumin da ya mika hadayar. AT: "daga gare ku".