ha_tn/mal/02/10.md

2.3 KiB

Muhimmin Bayani:

A na, annabi Malakai ya fara magana ga 'yan'uwasa Isra'ilawa.

Ashe, ba dukkanmu ubanmu daya ba ne? Ba Allahn nan daya ya hallice mu ba?

Malakai ya yi wadannan tambayoyi don ya tunasar da 'yan'uwansa Isra'ilawa game da abin da suka riga suka sani. AT: "Dukkanku kun sani cewa dukkanmu ubanmu daya ne, cewa Allah ya hallici al'umma ta wurinmu" ko "Dukkanku kun sani cewa Allah ne uban dukkanmu Isra'ilawa, domin shi ne ya hada al'ummarmu".

Ba Allahn nan daya ya hallice mu ba?

An nfi wannan tambayar don ta bayyana wata magana. AT: "Hakika, Allah daya ne ya hallice mu".

hallice mu

Mai yiwuwa wannan yana nufin yadda Allah ya hada Ibraniyawa suka zama al'umma.

Me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin kakanninmu?

Malakai ya yi wannan tambayar domin ya tsauta wa 'yan'uwansa Isra'ilawa. Za a iya bayyana wannan tambayar a matsayin magana. A.T: "Bai kamata mu yi wa juna keta ba, ko mu raina alkawarin Allah ta wurin rashin biyayya da umurninsa, kamar yadda kuka yi".

Yahuza ta keta alkawari

A nan, "Yahuda", tana nufin mutanen da ke yankin Yahuda, kuma ana maganar yadda suka keta alkawarinsu da Yahweh kamar su mutum daya ne mai suna "Yahuzd". AT: "Mutanen Yahuda suna rashin aminci".

An aikata mugun abu a Isra'ila, da a Yerusalem

Za a iya fadin wannan kai tsaye. AT: "Mutane suna aikata ayyukan assha a Isra'ila da Yerusalem".

Gama Yahuda ta kazantar da tsattsarkar wuri na Yahweh

A nan, "Yahuda" kuma tana nufin jama'ar Isra'ila. AT: "Gama jama'ar Yahuda sun kazantar da wuri mai tsarki na Yahweh".

auro matan da suke bauta wa wani allah

An sake magana kan mutanen Yahuza kuma kamar mutum daya ne mai suna "Yahuda". A.T: "ya auro mata daga wadansu al'ummai, matan da suke bauta wa gumaka".

Bari Yahweh ya kawar da mutumin da ... daga alfarwar Yakubu

Akan yi maganar hallaka abu kamar kawar da shi daga wani abu. AT: "Bari Yahweh ya hallaka kowane mutum a alfarwar Yakubu wanda ..." ko "Bari Yahweh ya kashe duk wani a al'ummar Isra'ila wanda ..."

alfarwar Yakubu

A nan "alfarwar Yakubu" tana nufin al'ummar Isra'ila.

Yakubu

A nan, "Yakubu" yana nufin dukkan Isra'ila, domin Yakubu yana daya daga cikin kakannin da Isra'ilawa suka samo asalin zuriyarsu.

wanda ya farka, da wanda ya amsa

Kamar wannan furcin yana nufin "kowane mutum".