ha_tn/mal/02/08.md

1.1 KiB

kun kaunce daga hanya

Ana maganar irin halin da ya kamata a nuna kamar madaidaiciyar hanyar da ya kamata a bi ne, sa'anna watsar da halayyara kirki kuma ana maganarta kamar juyawa daga wannan hanyar.

Kun sa mutane da yawa sun yi tuntube

Ana maganar rashin biyayya ga Allah kamar tuntube.

Kun sa mutane da yawa sun yi tuntube game da doka

Wannan furcin, "game da doka", yana bayyana yanayin "tuntuben". AT: "Kun sa mutane da yawa sun yi rashin biyayya ga doka".

a gaban dukkan mutane

Wannan maganar tana nufin yadda mutane suke sane da mugayen halayen firistoci.

kiyaye hanyoyina

A nan, "hanyoyi", tana nufin "nufi", da "halaye". Ana maganan wadannan hanyoyin kamar abubuwa ne da za a iya ajiyewa a kiyaye. AT: "bi nufina game da yadda ya kamata ku yi rayuwa".

nuna sonkai game da doka

"saukaka wa wadansu ka'aidar da ya kamata a bi don mutanen da kake so, sa'adda tsananta ka'idar da za a bi don mutanen da ba ka so".

nuna sonkai

A nan, ana maganar halin nuna wa wadansu mutane alfarma fiye da sauran kamar wani abu ne da za a iya nuna wa wadansu. AT: "sanar da mutane cewa kuna nuna wa wadansu alfarma fiye da sauran".