ha_tn/mal/02/05.md

1.7 KiB
Raw Permalink Blame History

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana da kabilar Lebi su mutum daya ne.

Alƙawarina da na yi da shi na rai da salama ne

A nan, ana maganar sakamakon alkawarin da ake sa ran samu kamar alkawarin ne kansa. AT: "Manufar alkawarina da Lebi ita ce don firistoci su yi zaman wadata da salama".

ji tsorona, yana kuwa tsorona

Wannan furcin ya ci gaba da misalin nan, amma bai bayyana wani ra'ayi da aka nufa a nassin ba. AT: "Alƙawarina da shi kuma tsoro ne, ya kuwa ji tsorona" ko "Cikin alƙawarina da shi, na bukace shi ya ji tsorona, ya kuwa ji tsorona".

tsoron sunana

A nan, "sunana", yana nufin Allah kansa.

ba a sami karya a bakinsa ba

A nan, samun wani abu yana nufin akwai abin. AT: "babu karya".

a bakinsa

A nan, "bakinsa" yana nufin iyawar mutum ta yin magana.

Ya yi tafiya tare da ni

A nan, tafiya tana nufin rayuwa, tafiyar da rayuwar mutum a wata hanya ta musamman.

da salama da gaskiya

A nan, bayanin yana nuna halin da Lawi ya yi rayuwa. AT: "cikin salama da gaskiya".

Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta

A nan, ana maganar shawo kan mutane daga aikata zunubi kamar an juya su ne daga zunubi. AT: "ya shawo kan mutane da yawa su daina zunubi".

Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi

A na, ana maganar ilimi kamar wani abu ne da firist zai iya ajiyewa. A wannan nassin, maganar "kiyaye ilimi" tana nufin sadar da gaskiyar sani game da Allah.

lebuna

A nan "lebuna" suna nufin iyawar mutum ta yin magana.

bidi ilimi

"marmarin samun umurni"

bidi ilimi

A nan, ana maganar ilimi kamar wani abu ne da mutane za su iya nema. AT: "neman firist don ya koyar da su da gaske".

daga bakinsa

A nan, "baki" yana nufin abin da mutum yake fada.