ha_tn/mal/02/03.md

1.5 KiB

zan watsa kashin dabbobi a fuskarku

A nan, "kashin dabbobi a fuskarku", tana nufin kunyatarwa. AT: "Hakika, zan jefa ku cikin kunya; za ta yi muni kamar watsa kashin dabbobi a fuskarku".

kashin dabbobin bukukuwanku

A nan, "bukukuwa", suna nufin dabbobin da firistoci suke mikawa hadaya a bukukuwa Isra'ilawa. Mai yiwuwa "kashin dabbar" tana nufin kashin da dabbobin suke yi dab kamin a yanka su don hadaya, da kuma kashin da ake samu a cikin dabbara sa'adda ake yayyaka namansu kamin a mika su hadaya. Ma'aikatan haikalai suka kai wannan kashin dabbar zuwa wani wuri a wajen haikalin, watakila ma a wajen Yerusalem.

kuma zai tafi da ku tare da shi

Za a iya fassara wannan mawuyacin furcin a matsayin "kuma Allah zai tfi da ku tare da shi", wato, tare da kashin dabbobin. Wannan furcin yana ci gaba da misalin yanka dabbobi don hadaya, kuma za a iya fadinsa a kai tsaye. A.T: "kuma za a jefar da ku a kan tarin kashin dabbobin; Allah zai tabbatar cewa an dauke ku sa'adda ake cire dukkan kashin dabbobin".

zai tafi da ku tare da shi

Ma'anar wannan maganar tana iya zama 1) Allah zai hukunta firistocin da suka yi rashin aminci ta wurin kashe su, da kuma sa wa a dauke jikunansu a jefa a kan kashin dabbobin, ko 2) Allah zai hukunta firistoci marasa aminci a wata mumunar hanyar da zai zama kamar an kawar da gawawwakinsu tare da kashin dabbobin.

Lebi

Yahweh yana maganar Lebi kamar shi daidai ne da zuriyarsa, wato, kabilar Lebi. AT: "domin alkawarina ya kasance tare da ku, zuriyar Lebi".