1.8 KiB
Sa'ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku mika mini hadaya, wannan ba mugunta ba ce?
A nan, Yahweh yana yin tambaya don fadin wani abu. Wannan maganar tana a matsayin tsautarwa ga mutanen. AT: "Kun sani sosai cewa mugunta ce a gare ku ku mika makauniyar dabba don hadaya!"
Sa'adda kuka mika gurguwar dabba, mara lafiya, wannan ba mugunta ba ce?
A nan, Yahweh yana yin tambaya don fadin wata magana. AT: "Kun sani kuma sosai cewa mugunta ce a gare ku ku mika gurguwar dabba, mara lafiya!"
Ku ba mai mulkinku irin wannan!
A nan, Yahweh yana ba da umurni don bayyana wani musalin. AT: "Idan kun mika irin wannan wa mai mulkinku"
Zai karbe ku, ko zai fifita ku?
A nan, Yahweh yana yin wannan tambayar domin ya tsautar wa mutanen. AT: "Idan kun yi wadannan abubuwan, kun sani mai mulkinku ba zai amince da ku ba. Ba za ku sami tagomashi a wurinsa ba".
zai fifita ku?
Fifita mutum yana nufin karbar mutumin da nuna masa tagomashi. AT: "zai karbe ku da tagomashi?" ko "zai yarda ya taimake ku?".
Ba ko Mika
A bayar a matsayin kyauta don nuna bangirma.
Yanzu kuna ta bdar fuskar Allah, domin ya nuna mana alheri
Yanzu Malakai ba ya magana a madadin Allah. Yana magana kai tsaye da Isra'ilawa; yana sukar lamirinsu don tunaninsu cewa Allah zai nuna musu jinkai.
kuna ta bidar fuskar Allah
A nan, "fuska", tana nufin Allah da kuma kasancewarsa. AT: "kuna ta bidar Allah a gabansa"
da irin wannan hadayar a hannunku, zai fifita waninku?
A nan, Yahweh yana yin tambaya domin ya fadi kalmar tsautarwa. AT: "idan kun mika hadayu marasa karbuwa, hakika, Allah ba zai fifita ku ba".
da irin wannan hadaya a hannunku
A ibraniyanci an fassara wannan mawuyacin kalma a hanyoyi dabam-dabam a sabobbin juyi.
a hannunku
A na, "hannu", yana nufin yadda mutane suke kawo hadayu. AT: "wadda kuke kawowa"