ha_tn/mal/01/01.md

1.8 KiB

Shelar kalmar Yahweh ga Isra'ila ta wurin Malakai

Za a iya furta wannan kamar magana. "Wannan shi ne shelar maganar Yahweh ga Isra'ila, wanda ya yi ta hannun Malakai"

Yahweh

Wannan shi ne sunan Allah, wana ya bayyana wa mutanensa a Tsohon Alƙawari. Duba shafin fassaraKalma game a kan Yahweh game da yadda za a fassara wannan.

ta hannun Malakai

A nan, "hannu", yana nufin aiki ko aikatawa. AT: "ta wurin ayyukan Malakai"

Ta yaya kake kaunarmu?

Wannan tambayar tana nuna cewa mutanen suna shakkar abin da Allah yake fada. Za a iya fadin wannan a matsayin magana. AT: "Ba ka nuna cewa kana kaunarmu ba".

Ashe Isuwa ba dan'uwan Yakubu ba ne?

Wannan tambayar, wadda amsar Yahweh ce don tuna wa jama'ar tarihin kasarsu, za a iya furta ta kuma kamar magana. AT: "Kun sani Isuwa dan'uwan Yakubu ne".

Yahweh yace

"Yahweh ya fadi wannan"

Yakubu nake kauna

A nan, "kauna", tana nufin dangantakar biyayya tsakanin Yahweh da Yakubu, inda aka sami alkawari a tsakaninsu. Za a iya fadin wannan kai tsaye. AT: "kamar yadda kuka sani, na mika kaina ga alƙawarin kaunar Yakubu".

Yakubu nake kauna

A nan, wannan sunan, "Yakubu", ba ga Yakubu kadai yake nufi ba, amma dukkan zuriyarsa.

Na ki Isuwa

A nan, "ki", yana nufin cewa babu alkawari tsakanin Yahweh da Isuwa. Amma, ba ya nufin cewa Yahweh yana da wata kiyayya a zuciyarsa game da Isuwa.

Na ki Isuwa

Sunan nan, "Isuwa", ba yana nufin Isuwa ba kadai, amma dukkan zuriyarsa.

tuddansa

Wannan yana nufin kasar kan tudu ta Idom.

na maida gadosa wurin zaman namun jeji

A Tsohon Alƙawari, kasancewar namomin jeji kamar diloli abu ne da akan mora do bayyana kasar da mutane suka zauna a ciki a da, amma suka watse suka bar ta, ta zama kango.

gadonsa ko kuma kasarsa

A nan, "gado", yana nufin yankin kasa ta zuriyar Isuwa, kasar Idom, wadda aka mamaye.