ha_tn/lam/02/11.md

806 B

Hawayen idanuwana sun gaji da zubowa

Wannan karin magana ne. AT: "na yi kuka har sai da na kasa iya yin kuka kuma" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

cikina ya kiɗime

Kalman nan "kiɗime" na nufin tafiya a kewaye cikin rikici, kullum a juyawar siffar zobe. Wannan baya nufin cewa a zahiri ciki na kiɗimewa, amma na bayyana yadda marubucin yake ji. AT: "ciki na na ciwo" "ciki na yi mani zafi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ina hatsi da ruwan inabi?

Wannan tambaya ce da ke roƙon wani abinda za'a ci. Yaran suna faɗa wa mamarsu cewa suna jin yunwa. Wannan kalmar "hatsi da ruwan inabi" hanya ce ta cewa abinci da abin sha. AT: "Ka bamu wani abu mu ci mu sha. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])