ha_tn/lam/02/01.md

1.1 KiB
Raw Permalink Blame History

Muhimmim Bayani:

Sabuwar waka ya fara. Marubucin Makoki yayi amfani da hanyoyi daban-daban domin ya nuna yadda mutanen sun rasa tagomashi daga wurin Allah. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/writing-poetry]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ubangiji yã rufe ɗiyar Sihiyona a karkashin gizagizan fushinsa

Wannan yana maganar fushin Yahweh a kan Yersalem. Manufar na iya zama 1) Allah ya so ya kawo bala'i ga mazauna Yerusalem ko 2) Allah ya rigaya ya cutar da mutanen. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor).

Ya jefar da darajar Isra'ila ƙasa daga sama zuwa duniya

Wannan magana "darajar Israila" na nufin Yerusalem. Wannan shafi na magana a kan mutanen Yerusalem sun rasa tagomashi daga Ubangiji kamar an jefa su ne daga gaban sa. Maganar nan "daga sama zuwa duniya" babban nisa ne da ke wakiltar yawan rashin tagomashin= daga Ubangiji. AT: " Yerusalem, darajar Israila, ta rasa dukan tagomashi da Ubangiji" or "Yerusalem ta rasa dukan tagomashi daga Ubangiji" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]])