1.1 KiB
A kwanakin ƙuncinta da rashin wurin zamanta
"A lokacin ƙuncinta da rashin wurin zamanta"
Yerusalem zata kira ga zuciya
A nan "Yerushalima" na maganar mutanen da ke zama a can. Maganar nan "kira ga zuciya" wata karin magana ce. AT: "mutanen Yerusalem za su tuna" ko "Yerusalem za su tuna" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]])
dukiyoyinta masu kyau
Wannan na nufin arzikinsu masu kyau.
a kwanakin dã
"a dã." Wannan na nufin lokaci kafin a kama mutanen Yerusalem. AT: "kafin bala'in ya faru" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)
Sa'ad da mutanenta suka faɗi a hannun abokan gãba
Kalmar nan "hannu" na nufin sojojin abokan gaba. AT: "Lokacin da magabci ya ci nasara ya kuma kama mutanenta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)
sun gan ta sun kuma yi dariya
Wannan yana nuna cewa sun yi murna da yi wa Yerusalem ba'a lokacin da aka lalata ta.
ga hallakarta
Za a iya bayyana wannan kalma "hallaka" a aikace. AT: "saboda ta halaka" ko kuma "yayin da suka halaka ta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)