ha_tn/lam/01/01.md

1.4 KiB

Muhimmim Bayyani:

An yi amfani da nau'ikan karin waƙoƙi a cikin wannan littafin. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/writing-poetry]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ta

Marubucin Makoki ya rubuta game da birnin Yerusalem kamar mace ce. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

kamar gwauruwa

Wannan jumla tana kwatanta Yerusalem da macen da ba ta da kariya saboda mijinta ya mutu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

Dã gimbiya ce a cikin al'ummai

Wannan na magana ne a kan Yerushalima da aka girmama kamar ita gimbiya ce. AT: "Da ita kamar gimbiya ce a cikin al'ummai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

an sa ta aikin bauta na dole

"an maida da ita baiwa ta dole" Za a iya juya wannan a aikace. AT: "amma yanzu ta zama baiwa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Tana kuka da koke-koke

Marubucin ya bayyana Yerusalem kamar ta na da motsin zuciya kamar mutum. Birnin kuma na tsaye a matsayin mazaunanta. AT: "mazaunan birnin suna kuka da makoki ... kuma hawayen su ya rufe kuncin su" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-personification]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]])

kuka da koke-koke

Kalmar nan "kuka" da koke-koke wat nishi da mutun yakan yi idan yana kuka da ƙarfi. AT: "kuka da karfi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)